Alúmomin Philliphines sun fara kada kuri’a a zaben shugaban kasa

Al’umar Philippines na gudanar da zaben shugaban kasa, inda ake sa ran wani maganannen Magajin-gari, wato Rodrigo Duterte zai kasance shugaban kasa.

Rodrigo Duterte dai ya samu dimbin magoya baya a yakin neman zabensa.

Rahotanni sun ce Rodrigo Duterte mutum ne mai yawan takaddama, ba ya shakkar magana, kuma manufofinsa cike suke da tawili.

Ya dai yi barazanar halaka dubban masu aikata miyagun laifuka, ya kuma ce zai taka kowa tamkar mai kama-karya idan ‘yan majalisar dokokin kasar suka ki yi masa biyayya.

Har-wa-yau ya shaida wa magoya bayansa cewa kula da Farka ko Farekunsa ba za ta zame wa gwamnati dawainiya ba, saboda gidajen da yake ajiye su ba masu tsada ba ne.

A halin da ake ciki dai shi ne mafi tagomashi ko farin-jini a tsakanin sauran abokan hamayyarsa mutum hudu, koda yake ya yi zargin cewa gwamnatin kasar na shirin tabka magudi wajen ganin dantakaranta, Mar Roxas ya ci zaben.

 

Abdulkarim Rabiu.