Amnesty ta soki yarjejeniyar EU ta Turkiyya

Kungiyar kare hakkin biládama ta kasa da kasa ta yi kira ga Kungiyar Tarayyar Turai EU da ta dakatar da shirinta na mayar da ‘yan gudun hijira da ke neman mafaka zuwa kasar Turkiyya.

 

Kungiyar mai fafutukar kare hakkin al’umma ta yi wannan roko ne a cikin wani bayani da ta gabatar mai shafuka 35, inda ta ce wannan mataki na EU bai dace ba domin ya sabawa ka’ida.

 

A yanzu haka dai kasar Turkiyya na zama mai masaukin ‘yan gudun hijira miliyan 3, da suka hadar da ‘yan Siriya miliyan 2.75, kuma tana sa ran samun karin wasu bisa ga yarjejeniyar da Turkiyyan ta cimma da Tarayyar Turai.

 

Yarjejeniyar dai ta tanadi cewar dukkan ‘yan gudun hijira da suka isa tibirin Girka bayan ranar 20 ga watan Maris, za’a tasa keyarsu zuwa Turkiyya.

 

DW/Abdulkarim Rabiu