Amurka Ta Kakabawa Kwamandan ‘Yansandan Birnin Kinshasha Takunkumi

Amurka ta sa takunkumi ga babban jami’in rundunar ‘yan sandan birnin Kinshasa na Jamhuriya Demokaradiyyar Congo, sakamakon tada hankali da kuma kashe wasu fararen hula.

 

Daga yanzu dukkan wasu kaddarori da suke mallakar Celestin Kanyama ne dake Amurka an kulle su, haka kuma an hana Amurkawa yin duk wata harkan kasuwanci da shi.

 

Amurka ta soki lamirin Kanyama ne shi da ‘yansandan sa na sanya tsoro ga ‘yan kasar ta Jamhuriyar Demokaradiyyar Congo, domin kawai kasar ta kusa gudanar da zaben shugaban kasa cikin watan Disamba.

 

Ana tuhumar shugaban kasar Joseph Kabila da kokarin sake dokokin zaben kasar domin ya samu damar sake tsayawa takara zagaye na 3, wanda kuma yin haka tamkar yi wa dokar kasar karan tsaye ne.

 

Gwamnatin Shugaba Obama tace rundunar ‘yan sandan da Kanyama yake jagoranta tayi anfani da tashe-tashen hankula domin ganin ta durkusad da wadanda basa ra’ayin shugaba Kabila ciki kuwa harda mata da yara wanda haka yayi dalilin mutuwar mutane 40.

 

‘Yansanda sun kai samame a gidaje da dama a cikin birnin Kinshasa, inda suke fito da mutane da karfi da yaji, musammam wadanda suke tuhumar cewa basa goyon bayan shugaba Kabila, suna musu barazanar kashe su, wasun ma sun kashe su.

 

 

VOA/Abdulkarim