An baiwa dakarun Najeriya horo na hadin gwiwa da sojojin Birtaniyya.

Rundunar sojin Najeriya ta ce makasudin wannan horo na hadin gwiwa da dakarun Birtaniya shi ne don koya wa sojojin dabarun yaki na zamani.

Shugaban rundunar sojin Najeriya Janar Tukur Buratai ne ya sanar da hakan yayin da yake bayani a wajen bikin yaye sabbin kuratan sojoji karo na 74 da ya gudana makarantar sojoji dake birnin Zaria, jihar Kaduna dake arewa maso yammacin Najeriya.

Janar Buratai wanda babban jami’an gudanarwar Rundunar sojin Najeriya Manjo Janar A. B. Abubakar ya wakilta ya ce, “ An bullo da shirin horon sojoji na hadin gwiwa da dakarun Birtaniya ne da nufin koyar dasu dabarun yaki na zamani.

‘’An yi hakan ne don tabbatar da kun koyi dabarun yaki irin na zamani da kuma wayar da kai akan abubuwa masu fashewa da kuma dabarun yadda mutun zai tsira da ransa domin ku zama hadaddiyar rundunar soji mai karfin da za ta iya tunkarar duk wata barazanar tsaro.’’

A cewar shugaban rundunar sojin Najeriyar, wannan horo na da mutukar mahimmanci musamman ma idan aka yi la’akari da kalubalen tsaron da yanzu haka kasar ta ke fuskanta.

Har-wa-yau ya bukaci sabbin kuratan sojojin da su kasance masu biyayya, da kamun kai, da da’a da kuma girmamma juna.

Kazalika Buratai ya shawarce su da su yi amfani da horon da aka basu a wuraren da aka tura su aiki.

Ya kara da cewa nan bada jima wa ba kalubalen tsaron da kasar ta ke fuskanta zai zama tarihi, yayin da ake daukar kwararan matakan da suka wajaba domin cimma nasara.

“Bikin wannan rana wani mahimmin tarihi ne ga makarantar sojoji dake Zaria da ma Najeriya baki daya.

‘’ An kafa wannan makaranta mai dunbun tarihi a shakarar 1924, kuma ta jima tana yaye zakakuran dakaru ga rundunar sojin Najeriya’’

“ makarantar na samar da matasan sojoji maza da mata da zasu kare martabar Najeriya da kuma fuskantar duk wata bazana,” A cewar Janar Buratai.
Janar Buratai ya yaba wa daukacin ma’aikatan makarantar sojojin bisa abin da ya bayyana a matsayin gagarumar nasara ta ko wane fanni na samar wa da sojoji horo.

Fiye da kuratan sojoji 2,900 a dauka a cikin shirin daukar sojoji karo na 74.

Abdulkarim Rabiu