An bukaci kafafan yada labarai da su rika amfani da dokar yancin yada labarai

An bukaci ka fafafan yada labarai da su rika amfani da dokar yancin fadin albarkacin baki yadda ya kamata domin bankado ayyukan cin hanci da rashawa yayin da suke gudanar da aikinsu na neman labarai.

Daraktan cibiyar ‘yan jarida ta kada da kasa, Lanre Arogundade, shi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka yi wa lakabi da ‘’fadin albakacin baki” , wanda cibiyar ta shirya a birnin Lagos dake kudu maso yammacin Najeriya, tare da hadin gwiwar sashen hurda da jama’a na ofishin jakadancin Amurka dake birnin na Lagos, karkashin wani shirin hadin gwiwa domin bayyana gudunmawar da kakafen yada labarai ke bayar wa wajen tabbar da adalci.

Ya ce an yanke shawarar maida hankali akan kafafan yada labarai su rika yin amfani da dokar fadin albarcin baki ne, sakamakon abubuwan da suke faruwa kwanannan a kasar wandanda da suke nuna cewar akwai sauran rina kaba a bangaren gudanar da gaskiya da adalci a Najeriya duk kuwa da cewa an samu canjin gwamnati kusan shekara daya kenan.

                  

‘’Abin takaici ne yadda zababbun shugabanni ko dai a majalisar dokoki ko ta zartarwa suke cikin duhu, har ila yau abin damuwa ne yadda har yarzu ake samun yaduwar cin hanci da rashawa a fannin hadahadar mai’’ in ji Lanre Arogundade

Kazalika ya buka ci manema labarai da su rika amfani da dokar yancin yada labaran wadda ta zama doka shekaru uku da suka gabata, da kuma aka yi imani da cewar samar da ita zai share fage ga mahuntan da suke wakiltar jama’a su rika gudanar da ayyukansu cikin da gaskiya da adalci .

 

Abdulkarim Rabiu