An bukaci ma’aikatan sharia su goyi bayan shirin yaki da cin hanci.

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa EFCC, ta bukaci ma’aikatan sharia da su hada hannu da hukumar a yakin da take yi na kawar da cin hanci da rashawa a Najeriya.

Mai rikon mukamin shugaban hukumar ta EFCC Mr Ibrahim Magu ne ya yi wannan kiran a wajen bude taron karawa juna sani na yini daya wanda kungiyar lauyoyi ta kasa a Najeriya NBA tare da hadin gwiwar kwamitin shugaban kasa dake bayar da shawara kan yaki da cikin hanci da rashawa a Abuja babban birnin kasar.

A cewar Magu hukumar EFCC ba za ta iya kawar da cin hanki a Najeriya ba tare da hadin gwiwa duka masu ruwa da tsaki akan harkar ba , kazalika ya jaddada kokarin da yake yi na yaki da cin hanci  a Najeriya.

’’mun dauki kowa a matsayin mai ruwa da tsaki, EFCC ba ita ce kadai take da masaniyar yadda za a ci galabar masu ta’annatin da dukiyar gwamnati ba.

’’Ko kai ma’aikacin EFCC ne ko kuma  babban Lauya , nan bada jimawa ba za mu fara bincikar mutanen da suka sayi gidaje da kudaden sata da kuma wadanda suka taimaka musu su guji sharia’’. A cewar Mr Magu

Abdulkarim Rabiu