An cika shekaru biyu cur babu bullar Polio a Najeriya.

Najeriya na bikin cika shekaru biyu cur ba a sami bullar cutar shan inna ko Polia a kasar ba.

A wata sanarwa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu yace “ babban nasarar da zamu samu a nan gaba ita ce mu karbi takardar shedar rabuwa da cutar Polio a cikin shekara ta 2017 daga hannu Hukumar lafiya ta duniya wato WHO’’

“ yau mun cika shekaru biyu cur ba a kara samun bullar cutar Polio a Najeriya ba. Ina yi wa dukkan masu ruwa da tsaki murnar samun wannan nasara mai dubbun tarihi da kuma wadanda suka ci gaba da jajirwa domin tabbatar da cewar ba a kara samun bullar cutar polio a Najeriya ba’’, In ji shugaba Buhari.
Shugaban ya kara da cewa Najeriya tana hada hannu da gwamnatoci da kamfanini masu zaman kansu na kasa da kasa domin tabbatar da yaran Najeriya ba su kara kamuwa da cutar mai nakasar da mutane ba.

Ya ce akwai bukatar hada hannu domin tabbatar da kawar da cuyar kwata-kwata a Najeriya, ta hanyar fadada shirin yaki da cutar a kasashen dake Nahiyar Afrika, sannan ya umarci ma’aikatun lafiya, da yada labarai, da kuma wayar da kan jama’a da suka jajircewa wayar da kan al’umma domin tabbatar da karbar takardar shedar rabuwa da cutar a cikin shekara ta 2017.

Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da jajircewa domin tabbatar da hakan, ta hanyar bayar da goyan bayanta ta kowane fanni, da ci gaba da yin rigakafin cutar ta Poilo, da kuma yin garanbawul a bangaren kula da lafiya a matakin farko.

Shugaba Buhari ya kara da cewa zai ci gaba da yin iyakar kokarinsa don ganin an fitar da kudaden da ake bukata na aiwatar da shirin na kawar da cutar Polio a kan kari.

 

Abdulkarim Rabiu.