‘An gano tarkacen jirgin EgyptAir’

Rundunar sojin Masar ta ce an gano tarkacen EgyptAir wanda ya da ya fada tekun Bahar Rum ranar Alhamis.

Kasashen Girka da Masar da Faransa da kuma rundunar sojin Biritaniya ne suka kaddamar da gagarumin bincike a kusa da tsibirin Karpathos da ke Girka domin yiwuwar gano jirgin.

Kakakin rundunar sojin Masar ya ce an gano tarkacen jirgin da wasu kayayyakin fasinjojin, kimanin kilomita 290 daga gabar tekun Alexandria na Masar.

Shi ma kamfanin EgyptAir ya tabbatar wa da anema labaraiĀ  cewa an gano tarkacen jirgin nasa.

Jirgin, mai lamba MS804, ya tashi ne daga Paris zuwa birnin Alkahira na kasar Masar dauke da fasinja 66 da kuma ma’aikatansa a lokacin da ya yi layar-zana.

Kasar Girka ta ce bayanan da ke nuna tafiyar jirgin, sun nuna cewa jirgin samfurin Airbus A320, ya yi ta jujjuyawa sannan ya fada a teku.

Masar ta ce mai yiwuwa ‘yan ta’adda ne suka harbo jirgin, ba wai matsalar na’ura ba.

 

BBC/Abdulkarim