An kai hari a dandalin Russell na birnin London

Wata mace ta rasa ran ta, ya yin da wasu mutane biyar suka jikkata a harin da wani matashi ya kai da wuka a tsakiyar birnin London.

‘Yan sanda sun yi amfani da na’urar da ake azabtar da mutum da wutar lantarki wajen cafke matashin mai shekaru 19, da ya kai harin a dandalin Russell.

‘Yan sandan sun kara da cewa binciken farko da aka yi kan harin ya nuna cewa matashin ya na da tabin hankali, amma duk da haka dole ne a binciki batun ta’addanci a dalilan da suka sanya aka kai harin.

Kakakin ‘yan sanda a birnin ya ce a yau Alhamis za a kara yawan jami’an tsaro a titunan birnin London.
BBC/Abdulkarim