An kammala taron bunkasa fasahar sadarwa na Afrika na 2016

A ranar Alhamis din nan ce aka rufe babban taron masu ruwa da tsaki na yini uku akan harkokin fasahar sadarwa da yada labarai na Afirka na 2016.

Kasashen Afrika tare da hadin gwiwar ma’aikatar sadarwar Najeriya da kamfanin Galaxy Backbone gami da wani kamfani na Ingila mai suna Extensia Company Limited da sauran wasu kamfanonin sadarwa ne suka shirya taron bunkasa harkar sadarwa na zamani a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.

Manufar taron dai ita ce karawa kasashen Afirka karfin gwiwa domin ganin sun rungumi harkar yada labarai da sadarwa na zamani, wadda kuma ta yi daidai da bukatar Gwamnatin Najeriya a kokarin da take na rage dogaro akan albarkatun man fetur zuwa wasu sassa na bunkasa rayuwar bil’adama.

Hon. Abdul’aziz Tijjani Mahmud shi ne babban mai taimakawa Gwamnan jihar Kano dake yankin Arewa maso yammacin Najeriya na musamman akan harkokin kimiyyar fasahar sadarwa ta zamani wato ICT, kana daya daga cikin mahalarta taron ya kuma bayyana wa Muryar Najeriya cewa hakika idan aka rungumi harkar fasahar zamani, to kuwa za a rage dogoro akan albarkatun man fetur.

Da ya juya batun jihohi kuwa, Babban mai taimaka wa Gwamnan jihar Kanon, yace tuni Gwamnatin jihar ta Kano ta rungumi harkar fasahar sadarwa ta zamani a inda ta horas da dumbin matasa a wannan fanni, kuma a halin da ake ciki yanzu gwamnatin jihar Kano ta na amfani da ilimin fasahar sadarwa wajen tantance ma’aikatanta, a don haka ya shawarci Gwamnatoci wajen ganin suma su bi sahun jihar ta Kano.

Hon. Abdulaziz ya hori masu amfani da kafafen sada zumunta na zamani da su guji yada labaran kanzon kurege musamman masu alaka da tsaro.

Taron dai ya sami halartar manyan baki dake ciki da wajen Najeriya da kuma wakilan wasu kamfanonin sadarwa, gami da wakilci daga gwamnatin tarayya da na sauran jihohi 36 dake kasar.

Abdulkarim Rabiu/Musa Aminu