An tashi taron Opec ba tare da cimma matsaya ba.

Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur a duniya ta gaza kaiwa ga cimma matsaya a dangane da takaita fitar da danyan man a kasuwanin duniya a yayin taron su a birnin Doha.

Dadaddiyar takun saka tsakanin Saudiyya da Iran da ke zama jigajigai a cikin kungiyar ta OPEC su ne suka kawo kiki-kaka a yunkurin da kungiyar take wajen takaita fitar da danyan man a kasuwannin duniya.

Tun da farkon fari dai, sai da kasar Iran ta fice daga zaman taron na birnin Doha, a inda ta yi kememe wajen kin takaita yawan adadin danyan man da take fitarwa tana mai cewar so take ta amfana da ribar fitar da danyan man kamar yadda wasu kasashen suka yi a lokacin da aka sanya mata takunkumi.

An dai yi hada-hadar danyan man a 2014 da kusan sama da dala dari ga kowacce ganga, a yayin da yanzu haka ya fadi warwar da kasa da dala 40 ga kowacce ganga.

A wani labarain kuma, Farashin mai ya faɗi a bayan taron ƙasashe masu arzikin man ya gaza rage yawan man da suke haƙowa, domin farfado da farashin man.

Cikin ‘yan awoyi, farashin man ya fadi da kashi biyar cikin dari a kasuwar duniya.
Tattaunawar ta fuskanci koma-baya ne saboda batun kace-nace da aka yi tsakanin Saudiyya da Iran.

Saudiyya ta ce ba za ta rage yawan man da take haƙowa ba sai Iran ma ta yarda ta yi hakan.

Amma Iran tana so ne ta sayar da mai sosai domin cin gajiyar janye mata takunkumin hana sayar da man da aka yi.

Ƙasashe masu arzikin mai sun yi fatan farfaɗo da farashi yayin taron.

 

Abdulkarim Rabiu