An yaba wa gwamnatin Najeriya a kokarin da take yi na ceto ‘yan matan Chibok

Mr Michel Arrion, EU Ambassador to Nigeria and Ecowas

A ranar sha hudu ga watan Afirilun nan ne ‘yan matan nan na Chibok da ‘yan kungiyar Boko Haram ta sace su suka cika shekaru biyu a hannun ‘yan ta’addan.

An dai sace ‘yan matan ne tun ranar sha hudu ga watan Afirulun shekar dubu biyu da sha hudu a makarantar Sakandire ta ‘yan mata dake garin Chibok a jihar Borno yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Malam Mannir Dan Ali shi ne Shugaban kamfanin jaridar Daily Trust kana babban Editan Jaridar Aminiya da kuma takwararta ta turanci wato Daily Trust, a wata tattaunawa da ya yi da Musa Aminu na gidan Rediyon Muryar Najeriya, yace babu wanda ya yi tsammanin cewa wannan al’amari zai kai kai shekaru biyu ba tare da an kubutar da wadannan ‘yan mata ba, amma a jajibarin wannan rana ta cikansu shekaru biyu an fito da wani faifan bidiyo dake nuna cewa waddanan yara suna raye.

“duk da ba a bari a kwashe daidai amma har yanzu iyayen yaran kada su cire rai da dawowar yaran su domin ci gaba da rayuwarsu kamar yadda suka saba’’ In ji Malam Mannir.

Shugaban kamfanin jaridar ya bada misalin wani da kwatankwancin haka ta faru da shi a kasar Amurka har na tsawon shekaru goma, amma daga bisani ya kubata.

Kazali, Ya bukaci iyayen ‘yan matan na chibok da sauran ‘yan Najeriya da su ci gaba da addu’oi wajen ganin an ceto wadannan dalibai na makarantar Chibok.

Fitaccen dan Jaridar ya bukaci abokan aikin shi manema labarai da su kasance masu azanci lokacin da suke hada rahotonin masu alaka da satar ‘yan matan Chibok din, domin sanyaya zukatar iyayen yaran kana ta haka ne kadai zai sa iyayen su ki cire tsammanin dawowan yaran nasu gida.

A karshe ya yaba wa dakarun sojin Najeriya gami da Gwamnatin tarayya da kuma ta jihar Borno bisa namijin kokarin da suke yi domin ganin an kubutar da daliban makarantar sakandiren na garin Chibok.

A wani labarin kuma, Ministan tsaron Najeriya, Mansur Dan Ali ya ce suna iya bakin kokarinsu wajen ceto ‘yan matan Chibok da Boko Haram ta sace su fiye da 200.
Mai magana da yawun ministan, Kanar Tukur Gusau, ya ce ministan ya bayyana cewar suna iya ƙoƙarinsu domin kubutar da ‘yan matan amma ba za su fadi irin matakan da suke dauka ba saboda halin tsaro.
Sai dai kuma ministan ya ce suna son ceto ‘yan matan ne da ransu kuma cikin koshin lafiya.

Musa Aminu/Abdulkarim Rabiu