An yankewa tsohon ministan noma na Masar daurin shekaru goma

A ranar litanin din nan ce aka yankewa Salah El-din Mahmud tsohon ministan Noma na kasar Masar daurin shekara goma a gidan yari bisa tuhumar da ake masa ta cin hanci da karbar rashawa.

Kotun yanke hukunci manyan laifuffuka ta kasar ta kama Helal da kudin kasar har fan miliyan daya da kuma manajansa Mohedin Qadah shi kuma fan dubu dari biyar bayan an kamasu da bayar da cin hanci domin mallakar samun lasisin kasa.

Rahotanni sun bayyana cewa Helal da Qadah hankalinsu bai tashi ba dangane da wannan hukuncin na kotu

Amma lauyan dake karesu Farid al-Deeb yace zasu daukaka kara.

Idan za a iya tunawa Helal an kama shi yan mintuna jim kadan bayan ya yi murabus a cikin watan satumba bisa zargin da ake masa na bayar da rashawa daga wani dankasuwa don bayar da lasisin wani fili.

Murtala Tukur