Rundunar’ Yansandan Ghana ta nesanta kanta daga shiga harkokin Siyasa

A Ghana speto janar na ‘yan sandan kasar, John Kudalor, yace jami’ai zasu kasance “yan ba ruwanmu,” a babban zaben a kasar da za’a yi cikin watan Nuwamban bana.

 

Sifeto Janar Kudalor, yayi magana ne a wani babban taro da jami’an rundunar da duka kwamandojinta a duk fadin kasar suka halarta. Taron ya maida hankali ne wajen tabbatar da shirin ‘Yansandan gabannin zaben shugaban kasa da ‘yan majalisa da kuma na kananan hukumomi.

 

Haka nan shugaban rundunar ‘Yansandan yayi kira ga ‘yan kasar, da wadanda zasu jefa kuri’a su nisanci tarzoma, su gudanar da harkokinsu cikin lumana a lokacinda ake gudanar da zabe.

 

Kakakin rundunar ‘Yansandan kasar Cephas Arthur ya dage cewa “yansanda suna gudanar da ayyukansu bisa adalci wajen tabbatarda doka ba tare da la’akari da ko wace jam’iyya bace take mulki tun lokacin da kasar ta koma tafarkin mulkin demokuradiya a 1992. Haka nan yace rundunar ta kara himma wajen horas da jami’anta.

 

A halin da ake ciki kuma, ‘yan kasar sun bayyana damuwa da ‘yan banga da jam’iyun siyasa suke dauka a zaman masu aikin tsaro lokacin zabe.

 

Ana zargin kungiyoyin da kaiwa ‘yan hamayya hare hare lokacin zabe. Saboda haka ministan harkokin cikin gidan kasar yayi kira ga ‘Yansanda su soke irin wadannan kunguyoyi.

 

VOA/Abdulkarim Rabiu.