Babu wani bankin Najeriya dake cikin matsala- CBN

Babban bankin Najeriya CBN ya yi watsi da rahotannin da suka yi nuni da cewa mai yiyuwa ne wasu bankunan kasar sun fuskanta ko kuma za su shiga cikin Matsala.

A wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba mai dauke da sa hannun mukaddashin Daratar hurda da Bankuna, Isaac Okorafor, ta karyata zargin cewa Bankin Skye yana fuskanatar Matsala, kuma ta bai wa jama’a tabbacin kariya ga kudadensu da suke a jiya a bankuna.

”CBN na farin cikin jaddada muku cewa wadannan jita-jita da kage-kage ba gaskiya ba ne, kuma ba sa nuni da halin da ko wane banki ko kuma duka kamfanonin hada-hadar kudade suke ciki.

’’domin kaucewa kokwanto, an kaddamar da sabon kwamitin gudanarwar bankin Skye ne da nufin bunkasa harkokinsa ta yadda ba zai kara gaza cimma sharuddan da aka gindaya masa ba.

“Bankin Skye baya fuskantar matsala haka ma sauran bankunan babu wanda ke cikin damuwa.’’ A cewar sanarwar ta babban banin Najeriyar.

Kazalika CBN ya bukaci jama’a da su yi watsi da wadannan rade-redin , yana mai cewa shairri ne kawai na wadanda ba sa son ci gaban tsarin bankunan Najeriya da tattalin arziki.

Har-ila-yau babban bankin ya gargadi mutane kada su tsorata su cire kudadensu daga ko wane banki.

Abdulkarim Rabiu.