Congo: Za a gurfanar da Katumbi gaban Kuliya

A Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo, mutumin da ake gani zai kasance dantakarar shugaban kasa a bangaren ‘yan adawa, Moise Katumbi, zai gurfana gaban Kuliya ranar Litinin sakamakon zarginsa da ake yi cewa yana amfani da sojojin-haya.

Lauyoyin Moise Katumbi, wanda har wa yau shi ne tsohon Gwamnan jihar Katanga mai arzikin ma’adinai, sun ce a ranar Asabar din da ta gabata ne aka ba shi sammaci, bayan sojojin da ke tsaron lafiyar shugaban kasa sun caje gidansa.

Mista Katumbi dai ya musanta tuhumar da ake masa, yana zargin cewa gwamnatin kasar ce ke neman shafa masa kashin-kaji a idon magoya bayansa.

Ofishin jakadancin Amurka da ke Kinshasa ma ya musanta wannan zargin da ake yi wa Mista Katumbi.

Tun a shekara ta 2001, wato shekara 15 kenan shugaba Joseph Kabila ke mulkin Jumhuriyar Demokuradiyyar Congo, kuma har yanzu bai ce zai sauka daga mukaminsa ba, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar.

 

Abdulkarim Rabiu