Dan Najeriya ya samu lambar yabo a jamaiar Qatar

Wani dan Najeriya Hafis Bello, ya sami lambar yabo mafi daraja a fannin gabatar da kasida a babban taron shekara-shakara na Jami’ar Hamid bin Khalifa dake Qatar.

Taken kasidar da Malam Bello ya gabatar a taron shi ne “tasirin sauyin rayuwa da kuma yadda ake zubar da shara a unguwannin da mutane ke zaune a kasar Qatar’’.

Taron dai ya gudana ne a ranar asabar 16 ga watan Afrilun 2016 a birnin Doha wanda ake yi wa lakabi da birnin ko kuma cibayar ilimi.

Kungiyar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje reshen kasar Qatar (NIDO), ta taya Malam Bello murna bisa wannan gagarumar nasara da ya samu. Bugu da kari wannan na daya daga cikin abin alfahrin da ‘yan Najeriya ke nuna wa a kasashen waje.

Kazalika kungiyar ta ‘yan Najeriya mazauna kasahen ketare reshin kasar Qatar, ta karfafa gwiwar sauran al’ummar Najeriya da su yi koyi da irin wadannan ayyukan kwazo na malam Hafisz Bello.
Abdulkarim Rabiu