G20 ta Sha Alwashin Farfado Da Tattalin Arzikin Duniya

Ministocin hada-hadar kudaden kasashe 20 mafi karfin tattalin arziki a duniya, sun sha alwashi habaka tattalin arzikin duniya, wanda suka ce yana tangaltangal wajen farfadowa a duniya.

Wakilan kasashen sun fidda sanarwar haka ne a yau Lahadi daga birnin Chengdu dake kasar Sin, a lokacin da suka kammala taron nasu na kwana biyu.

Cikin abinda suka tattauna a taron har da matakin fitar Birtaniya daga kungiyar kasashen Turai. Wanda suka ce hakan zai shafi tattalin arzikin duniya ta wata fuskar.

Duk da yake dai sun bayyana cewa, kasashen da suke membobin G20 din sun yi tsayuwar dakan yadda zasu tari lamarin na tangadin tattalin arziki.

Sanarwar ta bayan taron G20 ta jaddada kira ga muhimmancin rage yawan samar da karafan kere-kere wanda hakan ke sa kwararar karafa a kasuwar duniya.

Musamman yadda China da kawayenta suke sayarwa duniya karafa cikin saukin farashi.