Gwamnan jihar kano ya kaddamar da shirin tallafawa marayu

Gwamnan jihar kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da wani shiri na samar da ayyukan yi ga marayu 520 da suka fito daga kananan humomi 44 dake fadin jihar.

Karkashin shirin an bai wa marayu ashirin-ashirin daga kananan hukumomi 8 dake cikin kwaryar birnin kano ko wannensu Naira dubu ashirin, yayin da aka bai wa marayu goma-goma da suka fito daga sauran kananan hukumomi 36.

Da yake gabatar da jawabi ga wadanda suka amfana da shirin, gwamnan ya ce gwamnatinsa ta dukafa wajen inganta jindadin rayuwar yara marasa galihu.

Har-ila-yau gwamnan ya bayyana cewar an yi garanbawul akan dokar kula da marayu da jihar kano domin inganta tsaro da rayuwar marayu, ya ce kula da marayu wajibi ne kuma ibada ne a addinance.

kamar sauran yara, marayu ma suna da yancin samun ingantaccen matsuguni da ilimi domin su bayar da gudunmawarsu wajen ci gaban kasa’’, in ji gwamnan Jihar, ya kara da cewa “su ma yara manya gobe ne”.

Kazalika, gwamnan ya bukaci masu hannu da shuni da su tallafawa ilimin marayu da kuma karfafa gwiwarsu su  zama masu fasaha  ta yadda za su iya bayar da gudunmawarsu wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.

Gwamnan ya kuma yi kira ga wadanda suke rike da marayu da kula da su yadda ya kamata, kuma su tabbata sun basu tarbiyya mai kyau ta yadda za su zama mutanen kirki.

Gwaman Ganduje ya kuma yi amfani damar kaddamar da wannan shirin wajen tallata kayan da ake samarwa a jihar Kano kana ya kaddamar da bikin makon kasuwanci a jihar ta Kano, wanda ma’aikatar kula da harkokin kasuwaci ta jihar ta shirya.

A wani labarin kuma, kimanin mutane 5,500 ne suka amfana da shirin bayar da magani kyauta na gidauniyar Ganduje tare da hadin gwiwar kungiyar bayar da tallafi ta Musulunci ta kasa da kasa (IIRO) a babban asibitin Murtala Muhammad dake birnin kano.

Gidauniyar Ganduje dai wani asusu ne na tallafa wa jama’a wanda gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kafa da nufin gudanar da ayyuakan jin kai ga wadan da basu da galihu.

 

 

Abdulkarim Rabiu