Gwamnan Jihar Kano Ya ‘Yanta Fursunoni 500

Yayin da ake tsaka da bukukuwan Sallah karama, Gwamnan jihar kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ‘yanta fursunoni 500 dake babban gidan yari na cikin kwaryar birnin kano, wadanda suka gaza biyan tarar da kotu ta sanya musu domin neman ‘yancinsu.

Gwamnan Kanon ya biya jimullar tarar Naira Miliyan 20 domin ‘yanta fursunonin, wadanda suka fito daga kananan hukumomin 44 dake daukacin jihar, kama daga Naira 20, 000 zuwa Naira 100,000.

Har-ila-yau gwamnan ya bai wa ko wannensu Naira 3,000 domin yin kudin motar komawa garuruwansu.

An saki fursunonin daga gidajen yari guda goma dake wurare daban-daban dake cikin jihar.

Jim kadan bayan Ganduje ya biya kudin belin fursunonin, ya shawarce su da su zama masu kyawawan dabi’u, kana ya jaddada cewar za a dauki wanda ke da sha’awar shiga shirin samar da ayyukan yi ga matasa aiki.

Ya ce an dauki wannan matakin ne bisa koyarwar Azumin watan Ramadan domin hada kan al’ummar Musulmi mai cike da tsoron Allah. Kana da rage cinkoso a gidaden kason dake fama da karancin ababen more rayuwa.

Da yake nasa jawabin Kwantrolan hukumar kula da gidaden jari a Jihar Kano, Ahmed Abubakar, ya yabawa gwamnan bisa taimakonsa na jin kai, inda ya bayyana cewa gwamna Ganduje ya na bayar da gudunmawa sosai wajen ci gaban gidanjen yarin jihar Kano fiye da yadda sauran hukumomin gwamnatin tarayya suke bayar wa.

Wasu fursunonin biyu da suma suna cikin wadanda suka samu ‘yanci Auwalu Adamu da Blessing Abbah, amadin sauran ‘yantattun fursunonin sun bayyana murnarsu da wannan al’amari, suka ce ba su taba tsammanin sunayensu zasu shiga cikin wadanda gwamnan zai fiya kudin yantasu ba.

Duka fursunonin dai sun yi alkawarin koma wa garuruwansu domin ci gaba da gudanar da al’amuransu na yau da kullum.
Abdulkarim Rabiu.