Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da umarnin daukar Karin dalibai a makarantar kwana ta marayu ta hadin gwiwa tsakanin kano da Borno.

Gwamnan jihar Kano dake arewa maso yammacin Najeriya, Datka Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da daukar Karin dalibai 100 da marayu wadanda rikicin Boko Haram ya daidai daga jihar Borno, domin samun guraben Karatu a makarantar hadin gwiwa tsakanin Jihohin Borno da Kano dake birnin Kano.

 

Gwamnan ya sanar hakan ne a ranar Laraba a birnin Kano yayin da yake karbar bakuncin tawagar wakilan gwamnati daga jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya karkashin jagorancin Kwamishiniyar kula da harkokin mata ta Jihar Borno Hajiya Fanta Baba Shehu.

 

“Saboda nasarar da makarantar da samu da daliban da aka fara da su guda 100, na tattauna da Gwamnan jihar Borno kuma ya amince ya karo mana Karin dalibai 100. Gwamnatin Kano za ta dauki nauyin karatun su har sai sun kammala karatun Jamiá’’ in Gwamna Ganduje

 

Dakta Ganduje ya kara da cewa gwamnatinsa ta gaji wannan makaranta ne daga gwamnatin da ta gabata Kana ta kara bunkasa ta da kayayyakin aiki, sannan ta bai wa kungiyoyin da ba na gwamnati ba damar bada tallafi ga makarantar, wanda hakan ya sa makaranta da zama zakaran gwajin dafi a birnin kano.

 

Gwamnan wanda nan take ya amsa bukatar Gwamnatin Jihar Borno da ta ne mi a bai wa dalibai 100 da aka fara dauka su kai ziyara Maiduguyi domin su ga iyayen da suke rikonsu, ya umarci shugabar tawagar wakilan na Jihar Borno ta sa hannu a kan takardar jarjeniyar dawo da daliban Kano cikin koshin lafiya bayan sun kammala hutun.

 

A nata bangaren, Kwamishiniyar Kula da harkokin mata ta Jihar Borno Hajiya Fanta Baba Shehu ta mika godiyarta ga gwamnatin Jihar kano bisa taimkakon jinkan da ta yi kana ta bukaci sauran gwamnatici da su yi ko yi da irin wadannan kyawawan dabiú.

 

Abdulkarim Rabiu.