Gwamnatin Jihar kano ta dauki nauyin dalibai 5400 don rubuta jarabawar shiga makarantun sakandare na tarayya

A wani yunkuri na bunkasa fannin ilimi, gwamnatin jihar kano dake arewa maso yammacin Najeriya ta dauki nauyin kimanin daliban makaratun firamare 5,400 dake fadin jihar domin rubuta jarabawar shiga marantun sakandare na tarayya.

Kafin wannan lokacin, daliban makarantun firamare na jihar Kano su na rubuta jarabawar shiga makarantun gaba da firamare da take basu damar shiga makarantun sakandare dake cikin jihar ne kadai.

Amma da zuwan wannan Gwamnatin ta Abdullahi Umar Ganduje, taga ya canacanta a kara wayar da kan daliban makarantun firamare na Jihar Kano don su rika rubuta jarabawar shiga makarantun sakandare na tarayya.

Idan za a iya tunawa a cinkin watan janairun shekarar nan da muke ciki ne, gwamnatin Jihar ta kafa wani kwamitin ilimi da nufin farfado da fannin ilimi a duka kananan hukumi 44 dake fadin jihar.

Hakan kuwa na daya daga cikin nasarar da gwamna Ganduje ya samu wajen bunkasa ilimi a fadin jihar.

 

Abdulkarim Rabiu