Gwamnatin Najeriya za ta kaddamar da Karin tauraron dan adam

Ministan Ma’aikatar sadarwa, Mista Adebayo Shittu ya bayyana cewar yanzu haka ana kokarin kaddamar da Karin taurarin dan adam guda biyu da za su bai wa maákatun Najeriya damar tattara bayanansu a cikin gida maimakon tattatara bayanai a kasashen waje.

Ministan ya bayyan hakan ne a wani taron jin ra’ayin jama’a da ma’aikatar yada labarai da al’adu ta shirya a Jihar Kaduna dake arewa maso yammacin Najeriya.

’’saboda tauraron dan adam daya kacal muke da shi, ya sa kamfanoni da dama suke tsoron za su iya hasarar bayanansu idan wani abu ya faru da shi’’ in ji Minista.

Ministan ya kara da cewar domin hada kan hanyoyin tattara bayanai a wuri guda, ya sa aka kaddamar da  kamfanin Galaxy backbone limited don samar da cibiyar tattara bayanai ga dukkan maáikatu, da hukumomi da sashe-sashe na gwamnatin tarayya.

’’ An samar da cibiyar ne domin adana bayanai na alámuran da gwamnatin tarayya take aiwatar wa a duk fadin kasar, kuma an alakanta ta da duka ma’aikatu, da hukumomi da sashe-sashe na gwamnatin tarayya’’. A ta bakinsa minista

A cewarsa, aikin wanda yanzu ana kan gudanar da shi zai lakume zunzurutun kudi har Naira miliyan dubu biyu, kuma da zarar an kammala zai bai wa gwamnati damar adana dukkan nin bayananta.

 

 

 

 

Abdukarim Rabiu.