Gwamnatin Najeriya za ta maida da hankali wajen samar da ababen more rayuwa

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewar tana mai da hanakali wajen samar da mahimman ababen more rayuwa domin bunkasa tattalin kasar wanda hakan na daya daga cikin tsarinta na fadada hanyoyin samun kudaden shiga.

Ministar kudi Mrs Kemi Adeosun ce ta bayyana hakan yayin da ta ke gabatar da jawabi ga mambobin majalisar dokokin kasar a matsayin wani bangare na muhawarar da yanzu haka ake yi da nufin farfado da tattalin arzikin kasar.

Mrs. Adeosun ta bayyana cewar Najeriya za ta maida hankali akan kudaden da ta ke kashewa wajen gudanar da manyan ayyuka  domin samar ci gaba mai dorewa ta fannin samun kudaden shiga da  kuma  bunkasa masanaántu da harkokin kasuwanci.

Ministar ta ce gwamnati za ta ci gaba da maida da hankali wajen samar da kudade ga hukumomin gwamnati domin aiwatar da kasasafin kudi na 2016, ya yinda kuma za ta bunkasa fannin ayyukan gona da sauran hanyoyin samun kudaden shiga da nufin habbaka tattalin arzikin kasar.

‘’Ba zan yi alkawarin kowa ce hukuma za ta sami addadin kudin da aka ware mata a cikin kasafin kudin ba. Kasafin kudi hasashe ne na kudaden da ake sa ran samu a shekara. Ya kamata Ma’aikatu da hukumomi da sashe-sashe na gwamnatin tarayya su mai da hankali wajen aiwatar da manyan ayyuka, kuma sai mun tattance mahimancisa kafin mu fitar da kudi’’. A cewarta.

Uwargida Adeosun ta kuma fadawa majalisar dokokin cewa ana kashe fiye da Naira miliyan dubu hudu wajen biyan kudin hayar hukumomi gwamntain tarayya daban-daban, amma ana kokarin mai da wadannan hukumomi zuwa wasu gine-gine da gwamnati ta kwato daga hannun wadanda suka yi sama da fadi da su a garuruwan Lagos da Abuja domin  rage kudaden da take kashewa.

A cikin bayanin nata, ministar ta ce za a tara Dala miliyan 4 zuwa 5 daga hukumomin da ba na gwamnati ba, ci kuwa hyarda hukumomin kasa da kasa da hukumomin da ke bayar da rancen kudi a kasashen ketare.

Abdulkarim Rabiu.