Gwamnatin Najeriya zata taimakawa jihohi aiwatar da kasafin kudi.

Gwamnatin Najeriya zata samar da rancen  Naira Miliyan dubu casaín don taikawa jihohin kasar aiwatar da kasafin kudi.

Wadannan kudade dai zasu taimakawa jihohi 36 dake kasar  aikawata da kasafin kudin cikin sauki.

Gwamnan jihar Akwa Ibom Mr Emmanuel Udom ne ya bayyana hakan  yayinda yake zantawa da manenma labarai bayan an kammala taron majalisar tattalin arziki ta kasa da ya gudana a Abuja babban birnin kasar.

A cewar gwamnan, gwamnnonin da suka halarci taron tattalin arzikin karo na 68 sun yin mutukar farin ciki da wannan bashin, wanda acewarsa za a dora kudin ruwa kashi 9 cikin 100.

ministar kudi ta yi wa taron bayani akan bashin kudi na Naira biliyan 90 na gwamnatin tarayyar kan kudin ruwa da ya kai kashi 9 cikin 100. Kawo yanzu jihohi biyar sun fara shirye-shiryen karbar bashin kudin da gwamnatin tarayya zata bai wa jihohin, wanda zai taimakawa musu biyan albashi, da alawus-alawus na ma’aikata. Ana sa ran saura jihohin ma zasu fara shirye-shiryen karbar bashin kudin,’’ in ji Gwmna Emmaneul

Mr Udom yace nan da mako mai zuwa idan Allah ya kai mu za a fara fitar da kudaden.

 

 

 

Abdulkarim Rabiu