Sarkin Marocco ya taya Shugaba Buhari Murnar dawo wa daga Landan

0
9

Mai martaba sarkin Marocco Muhammad na shida ya taya shugaban Najeriya Muhammadu Buhari murnar dawo wa hutun jinya daga birnin Landon.

A wata hira ta wayar tarho, sarkin Morocco ya bayyana farin cikinsa dangane da yadda ‘yan Najeriya suka tarbi Shugaba Buhari yayin da ya dawo gida Najeriya.

Ya ce ‘’alamu ne da ke nuni da cewa al’ummarsa na mutukar kaunar sa a matsayin shugaba’’

Sarki Muhammad na shida, wanda ya taba wata ziyarar aiki a Najeriya cikin watan Desamba, shi ma ya gayyaci shugaba Buhari domin ya kai masa irin wannan ziyara zuwa kasarsa Morocco.

Shugaban na Najeriya ya mika godiyarsa ga sarkin na Morocco dangane da kiran da ya yi masa ta wayar tarko domin ya ta ya shi murna dawo gida lafiya, da kuma ci gaba da karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

SHARE

bar sako