Kungiyar magoya bayan shugaba Buhari ta kai ziyara kudu maso gabas

0
6

Magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari karkashin jagorancin kungiyar dake mara masa baya wato Buhari Support Organisation (BOS) a turance ta yi wani tattaki domin ganewa idanunta irin ayyukan da yanzu haka gwamatin tarayya take gudanmar wa a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Tawagar wadda babban Daraktan Gidan Radiyon Muryar Najeriya (VON), Osita Okechukwu ya jagoranta tare da Shugaban gamayyar kungiyon dake goyon bayan gwamnati shugaba Buhari ta kasa, Mustafa Ahmed, ta kai ziyarar gani da ido a ayyukan tagwayen hanyoyin mota da suka tashi daga garurun Enugu zuwa Onisha da kuma wadda ta tashi daga Enugu zuwa Fatakwal.

Har ila yau a cikin tawagar akwai, Otumba Biodum Ajiboye, sakataren kungiyar, da shugaban matasa Okoro  Okoro da kuma babban jamaian gudanarwa na yankin Kudu maso gabas, Harris Ifeanyi Chukwu.

Da yake jawabi a wajen da ake gudanar da ayyukan, babban daraktan Muryar Najeriya, Osita Okechukwu, ya ce kungiyar ta yi wannan tattakin ne domin ganewa idanunta irin ayyukun da gwanatin tarayyar Najeriya ke gudanarwa a yankin kudu maso gabashin kasar, da nufin nuna irin ayyukan da shugaba Buhari yake yi a yankin.

’’ fitattun mutane da dama sun tuntube mu agame da dalilin wannan ziyara, amsar mu kuma shi ne mun gudanar da wannan ziyara ne domin mu gane wa idanunmu wadannan ayyuka, saboda lokaci yayi da alu’ummar kasa zasu nuna godiyarsu ga irin ayyukan da gwamnatin tarayya, da jihohi, da kananan hukumomin suke gudanarwa’’

A ra’ayinmu ci gaba da gudanar da manyan ayyuka it ce kadai hanyar da za a daina mantawa da manyan ayyukan da aka riga aka fara a wurare daban-daban duk kuwa da cewar an riga an sanya su a cikin kasasfin kudi,’’ in ji shugaban Muryar Najeriya

Babban daraktan Muryar Najeriya, Osita Okechukwu

Ya ci gaba da cewa abu na biyu shi ne muna so mu rika bibiyar masu kwantiragin ayyukan domin mu tabbatar suna gudanar da ayyukansu akan kari da kuma inganci.

 

Abdulkarim Rabiu.

 

 

SHARE

bar sako