Majalisar Dokoki ta Goyi Bayan Dangantakar Najeriya da Maroko

0
6

Majalisar dattawan Najeriya tace zata tabbatar da cewa anbi duk dokokin da suka dace na cimma nasarar kyakyawar hulda tsakanin Najeriya da kasar Maroko.

Shugaban Majalisar Bukola Saraki shine ya sanar da haka lokacin da ya gana da shugaban Majalisar kasar Maroko, Mr.Abdelhakim Benchamach a birnin Rabat.

Senata saraki ya yi nuni da ziyarar da Sarkin maroko ya kawo Najeriya inda yace an rattaba hannu akan yerjejeniya da dama tsakanin kasashen biyu a kan harkokin noma, makamshi, iskar gas da shinfida bututun iskar gas na yankin Sahara.

Saraki ya kara da cewa majalisar Dattawan ta yanke shawarar baiwa duk yarjejeniyar da aka rattaba hannu a kai kulawar gaggawa domin fara gudanar da aiki domin ci gaban tattalin arzikin kasa tare da bunkasa huldar arziki da sauran kasashen Afirka.

A nasa jawabi, Mr.El-Maliki yace tuni Sarki na Maroko ya kafa kwamiti da zai sanya ido domin tabbatar da yerjejeniyar da aka rattaba hannu ta fara aiki.

 

LADAN/ ABDULKARIM RABIU

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

SHARE

bar sako