NNPC Zai Dauki Matakan Samar da Isashshen Man Fetur a Najeriya

0
38

A ranar Lahadin nan ne Kanfanin man fetur na Najeriya NNPC ya sanar da cewa ya kammala dukkanin shirye-shiryensa na daukar matakan samar da isashshen man fetur a duk fadin kasar.

Kanfanin ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da babban manajan Daraktan hulda da jama’a na Kanfanin Mr. Ndu Ughamadu ya fitar a Abuja babban birnin kasar.

Sanarwar ta kuma ce daya daga cikin matakan da kanfanin ya dauka har da wasu dabarun shinfida bututun man Petur zuwa sassa daban daban.

Kanfanin yace a halin da ake ciki yana da liti sama da biliyan daya na man petur da zai wadatar da ababan hawa har na tsawon sama da wata daya a duk fadin kasar.

Sanarwar na ci gaba da cewa kanfanin zai fara sarrafa man Gas da man jirgin sama a nan cikin gida ba sai an fita dashi kasashen ketare ba.

 

Ladan/ Abdulkarim

 

 

SHARE

bar sako