Tattalin Arzikin Najeriya zai Bunkasa ta Fannin Noma

0
45

Mai taimakawa shugaba Najeriya kan harokin watsa  labarai na musamman Garba Shehu ya bayyana cewa kokarin da ake na fitar da Najeriya daga matsalar tabarbarewar tattalin arziki ya fara haifar  de ‘da mai ido, musamman a fannin ayyukan gona.

A cewar mai taimakawa shugaban kasar, karuwar shinkafar da ake samar wa da kuma sarrafa wa a fadin kasar ya riga ya sa an rage yawan musayar kudaden waje.

Shehu ya ce a cikin shekara ta 2015 kadai Najeriya ta shigo da tan 58,000 na shinkafa daga kasar Thailand a maimakon tan miliyan daya da dubu dari biyu a cikin shekara ta 2014.

Ya ce sakamakon karuwar noman shinkafa a cikin kasar da kuma shirin Babban Bankin Najeriya CBN na hana musayar kudaden da ake shigo wa da shinkafa daga kasashen waje, ya sa wasu kamfanonin sarrafa shirinfa na kasahen dake Nahiyar Asia rufe kamfanoninsu.

A cewarsa, hakan ya faru sakamakon Najeriya wadda na daya daga cikin kasashen duniya da suka fi shigo da shinkafa daga kasashen ketare ta daina siyan shinkafa daga wurinsu.

”Biyar daga cikin irin wadannan kanfanoni na kasar Thailand da suke sayar wa da Najeriya shinkafa sun daina sarrafata sakamakon janye sayan shinkafa da Najeriyar ta yi’’ In ji Garba Shehu

 

Abdulkarim Rabiu

bar sako