Najeriya Zata Fara Bikin Ranar Ruwa ta Duniya

0
38

Najeriya zata bi sahun sauran kasashen duniya wajen  bikin ranar ruwa ta duniya na shekara ta 2017  da wani tattaki na motsa jiki wanda Ministan albarkatun ruwa Sulaiman Adamu zai jagoranta, a ranar talata 21 ga watan Maris din 2017 a garin Abuja babban birnin kasar.

Ranar ruwa ta duniya dai biki da kasshen duniya ke yi a kowace  ranar 22 ga watan Maris duk shekara domin wayar da kan jamaa agamae da yadda ake kula da albarkatun ruwa da kuma nazarin irin ayyukan da fannin samar da ruwa yake yi.

Taken bikin na bana shi ne ‘’Ruwa da Gurbataccen ruwa’’ wato dangantakar dake tsakanin ruwa mai tsafta da gurbataccen ruwa a kokarin da ake yi na samar da ci gaba mai dorewa, da kuma hada karfi da karfe wuri daya don dore wa daga in da aka tsaya a bukukuwan ranar ruwa na duniya da aka gudanar a shekarun baya.

Kazalika bikin na bana zai taimaka wajen sanar da sabbin bayanai agame da yadda za iya amfani da gurbataccen ruwa wajen sarrafa shi ya zama wata hanya mai amfanai ta bunkasar tattalin arziki.

Musamman domin wayar da kan jama’a akan yadda za su rika sauya gurbataccen ruwa ya zama mai amfani a kowa ne bangare na Muradin samar da ci gaba mai dorewa da ya shafi albarkatun ruwa.

 

Abdulkarim Rabiu

 

bar sako