Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci kungiyoyi masu rike da makamai su aje makamansu

0
15
PIC.34. MEMBERS OF HOUSE OF REPRESENTATIVES AT A SPECIAL SITTING TO MARK END OF THE 2ND YEAR OF THE 7TH ASSEMBLY IN ABUJA ON THURSDAY (6/6/13).

Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci a kafa wata rundunar tsaro ta musamman domin gaggauta magance matasar masu rike da makamai dake yankunan jihohin Benue da Osun.

Wannan na daga cikin kudirin dokar da majalisar ta amince da su da aka gabatar agame da rikicin kabilanci da ya faru a garin Ile-Ife dake Jihar Osun da kuma hare-haren da aka kai kwanan akan wasu kauyikan dake jihar Benue.

‘Yan malajisun dai sun yi allawadai da wadannan hare-hare na jihohin Benue da Osun kana sun bukaci a kama tare da gurfanar da duk wadanda ke da hannu domin farfado da zaman lafiya a yankun da rikicin ya shafa.

Daga jihar Benue Mr Orker Jev , yayin da yake gabatar da kudirin dokar yace “mun yi allawadai da hare-haren masu rike da makamai suka kai  a kauyukan dake karamar hukumar Buruku dake cikin jihar Benue da kuma lalata amfanin gona, da kuma sace sacen kayyakin mazauna kauyuka wadanda  da ba su ji ba su gani ba.”

 

Abdulkarim Rabiu

SHARE

bar sako