Afghaistan: Harin masallaci ya yi sanadiyyar kisan mutane da yawa

0
176

Mutane 29 ne suka mutu inda wasu 64 suka jikkata sakamakon hare-haren bam 2 da aka kai a wani Masallacin Juma’a da ke garin Herat na Afganistan.

Mahukunta sun bayyana cewa, daya daga cikin maharan ya tayar da bam din da ke jikinsa a kofar shiga Masallacin tsakiyar garin Herat yayin da mahari na 2 kuma ya kutsa kai cikin Masallacin tare da bude wuta.

Bayan hare-haren Masallacin ya zama ba za a iya amfani da shi ba.

Haka zalika an bayyana fargabar yiwuwar samun karin wadanda za su mutu sakamakon harin.

Tun da fari mai Magana da yawun ma’aikatar kula da harkokin cikin gidan kasar ya bayyana cewa ya yi zargin wata kila an kai harin bom din a cikin wata mota ne.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta yi ikirarin daukar alhalin wannan hari, wanda ya faru a yankin da galibi Musulmai ne mabiya darikar Shia.

Abdulkarim

SHARE

LEAVE A REPLY