Al’umomin Kenya na jiran sakamakon babban zabe

0
73

Yayin da al’umomin Kenya ke jiran sakamakon babban zabe, shugabannin tawagar masu sa ido na kungiyar tarayyar Afrika, kana tsoffin shugabannin kasashe, da suka hada da Thabo Mbeki na Afrika ta kudu da John Mahama na Ghana sun bukaci al’umar kenya da su yi kokarin samun nasara gudanar da zaben ciki kwaciar akali da lumana.

Tsoffin shugabannin kasar dake jagorantar ayyukan sa ido a babban zaben na kasar kenya sun bukaci hakan yayin da ake shirin fara kada kuria.

Tun dai a jajiberen zaben ne Mr Mbeki a wani taron manema labarai ya bayyana cewa, suna da karfin gwiwa cewa za gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana, sai dai ya bayyana cewa dukkanninsu wato da shi da tsohon shugaban kasar Ghana John Mahama ba za su bar kasar a ranar 9 ga watan Agusta ba.

Ya ce akwai fargabar da zarar an  fadi sakamakon zabe rikici na iya barkewa a kasar ta Kenya kamar yadda ya faru a shekaru goma da suka gabata, sai dai ya bayar da tabbacin an dauke dukkannin matakan da suka wajaba na ganin an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.

Kazalika Mahama ya bukaci wadanda suka fadi zabe da su dangana ga Allah yayin da wadansu suka sami nasara su kuma a taya su murna.

Abdulkarim

 

 

 

 

 

 

 

 

SHARE

LEAVE A REPLY