Amurka ta nada mai bincike kan huldar Trump da Rasha

0
79

Mahukuntan  Amirka sun nada Robert Mueller da ke zama tsohon daraktan hukumar leken asiri ta kasa wato FBI, domin gudanar da bincike a kan zargin da ake na wata huldar kut da kut da ke akwai tsakanin wasu na hannnun damar Shugaba Trump da kuma kasar Rasha.

Mueller mutun ne da ya rike mukamin daraktan hukumar leken asiri ta kasa ta FBI daga shekara ta 2001 zuwa 2013 tun daga lokacin gwamnatin George W. Bush har zuwa ta Barack Obama.

Ya na da kima a idon Amirkawa a matsayin wani mataki na neman rage katsalandan din da gwamnatin kasar ke yi a cikin ayyukan binciken da hukumar ta FBI ke yi kan wannan batu na kusancin wasu na hannun damar Shugaba Trump da kasar Rasha.

Sai dai da yake mayar da martani ta shafinsa na tweeter kan nadin tsohon daraktan hukumar ta FBI, Shugaba Trump, ya ce ba shi da wata fargaba a game da sakamakon da binciken zai bayar domin yana da tabbacin babu wata alakar da ke da akwai tsakanin wasu na hannun damar tasa da kasar Rasha.

Abdulkarim/DW

SHARE

LEAVE A REPLY