An bukaci mata a Najeriya su rika shiga ayyukan noma

0
100

Wata hukuma mai gundanar da ayyukan sa kai ta kasar kanada da aka fi sani da “Cuso International” ta bukaci mata su rika shiga harkokin noma domin a dama da su.

An yanke shawarar hakan ne a wani taron sarakunan gargajiya da masu zuba jari da ya gudana a garin Kalaba, Babban birnin jihar Cross Rivers dake kudu maso kudancin Najeriya.

Da take gabatar da jawabi a wajen taron, masaniyar harkokin noma Folusho Olaniya ta bayyana damarmakin dake akwai na bunkasa ci gaban ayyukan goma a Jihar ta cross River.

a kwai damarmakin harkokin kasuwanci a albarkatun karkashin kasa da Allah ya huwace wa  jihar Cross River. Kuma damarmaki ne na bunkasa harkokin kasuwanci. Wadanda suke bukatar kware wa, da gogayya, kuma za su bai wa alummar jihar musamman ma mata damar cimma burinsu na rayuwa’’. In ji Olaniyan

A cewarta “Jihar cross River tana samar da kashi 12.5 cikin 100 na rogon da ake samar wa a Najeriya, da kashi 1.9 cikin 100 na manja, sai kashi 4.2 cikin dari na shinkafa da kuma kashi 19.8 cikin 100 koko da ya kai  akalla tan Miliyan uku da rabi.’’

Tace ta bangaren kiwon kifi da kaji kuwa, jihar za ta iya fadada shirin kiwon dabbobi ta hanyar karkafa gwiwar mata da yawa musamman matasa yan tsakanin shekaru 18 zuwa 35 su shiga fannin ayyukan gona.

 

Abdulkarim

 

 

SHARE

LEAVE A REPLY