An bukaci gwamnati ta sake nazari kan hana zirga-zirgar KEKE NAPEP a wasu sassa na Abuja

0
153

Kungiyar masu sana’ar tuka babura masu kafa uku da aka fi sani da KEKE NAPEP ta birnin Abuja, ta bukaci gwamnatin babban birnin tarayya da ta janje matakin hana su zirga-zirgar a wasu sassa daban daban na babban birnin.
Bayanin hakan ya ta fito ne daga bakin shugaban kungiyar, Hon. Alhassan Haske yayin da yake zantawa da manema labarai, a lokacin da tawagar kungiyar karkashin jagorancinsa suka kai ziyarar ban girma ga sarkin Hausawa mazauna garin Abuja Alhaji Umar Dan Gadima a fadarsa dake unguwar Gwarimpa.

Hon. Haske ya sana’ar KEKE NAPEP, sana’a ce mai matukar mahinmanci idan aka yi la’akari da irin gudun mawar da ta ke bayar wa wajen samar da aikin yi ga matasa da bunkasa tattalin arziki kana da kuma samar da kudaden shiga ga gwamnati. Adon haka akwai bukatar sake yin naziri akan wannan mataki da gwamntin birnin Abuja ta dauka na takaita sufurin babura masu kafa uku a wasu sasssa na birnin.

“Ina kira ga gwamnati da ta zauna da kungiyarmu domin tattauna yadda za a shawo kan wannan matsala”. In ji Hon. Haske.

Shi ma da yake nasa bayanin uban wannan kungiya kuma Sarkin Hausawa mazauna garin Abuja, Alhaji Umar Dan Galadima, ya ja kunnen masu sana’ar tuka babura masu kafa uku ne da su rika bin doka da oda, domin ta haka ne kadai za a sami kyakkyawar alaka a tsakanin gwamnati da masu wannan sana’a.

Ka zalika ya yi alkawarin zai yi iyakar kokarinsa wajen mika kokensu ga hukumomin da suka dace domin share musu hawayensu.

Idan ba a manta ba a cikin watan da ya gabata ne dai ma’aikatar babban birnin tarayya Abuja ta bayar da sanarwar hana zirga-zirgar babura masu kafa uku a wasu mahinman wurare dake birnin, matakin da yan kungiyar suke ganin ya kamata a sake yin nazari akai.

Abdulkarim Rabiu.

 

SHARE

LEAVE A REPLY