An bukaci gwamnatin Najeriya ta kara karfafa matakan tsaro a kasuwanni

0
94

An bukaci gwamnatin tarayyar Najeriya ta kara tsaurara matakan tsaro a kasuwanni domin kare lafiya da dukiyoyin jamaa.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Alhaji Hamisu Abubakar Jumare, babban dakartan kula da kanfanin gine-gine na Urban Shelters wato Urban Shelter Facility Management Company, kana mai kula da Kasuwar Garki ta kasa da kasa, a zantawarsu da Muryar Najeriya.

Alhaji Hamisu Abubakar Jumare yace tun lokaci da rikicin Boko Haram ya kunnu kai a Najeriya, su ka fara daukar tsauraran matakai a kasuwar Garki ta kasa da kasa domin kare lafiya da dukiyoyin jama’a.

Yace gwamnatin Muhmamadu Buhari ta yi namijin kokari wajen magance matalar tsaro da yankin arewa maso gabashin kasar ya jima yana fama da shi sakamakon ricikin ‘yan ta’addar Boko Haram, wanda ya yi sadiyyar rasa rayuka da dukiyoyin jamaa, yayin da da dama suka rasa matsugunansu.

Ya ce a matsayinsa na masanin harkar gine-gine akwai bukatar sauya fasalin ginin kasuwanni a kowa ne mataki na gwamnati ta yadda zasu rika tafiya da zamani, da katange su da kuma samar musu hayoyin shiga da fita tare da bincikar ababan hawa da dukkan mutanen da suke shiga da fita. A cewarsa ta hane kadai za a tabbatar da cikkaken tsaron lafiya da dukuyoyin jamaa a kasuwanni.

A karshe ya bukaci gwamnatin tarayyar Najeriya da ta kara karfafa matakan tsaro a dukkanninn kasuwannin dake Najeriya. Kazalika ya yi kira ga jamaa da su rika baiw a jamian tsaro goyan bayan a lokutan ta suke gudanar da aikin binke a kasuwannin.

Ana iya Sauraren cikakkiyar hira da Alhaji Hamisu Abubakar Jumare tare da Abdulkarim Rabiu

Abdulkarim.

 

 

SHARE

LEAVE A REPLY