An kashe sojojin kasar Sudan 2 a Yaman

0
66
Sojojin Sudan

Rundunar sojin kasar Sudan ta sanar da cewa, an kashe sojojinta biyu a yakin basasar da ake yi a kasar Yaman.

A wata sanarwar da kakakin rundunar sojin Birgediya Ahmad Khalifa Alshami ya fitar ya bayyana cewa, dakarun Sudan sun kai farmakai da yawa a ranakun Juma’a da Asabar din da suka gabata a wani bangare na taimaka wa Kungiyar Kasashen Larabawa.

Kakakin ya ce, a yayin farmakan an kashe sojojin Sudan 2 tare da jikkata wasu da dama.

Kakakin na sojojin bai bayyana takaimaiman a yaushe ne aka kashe sojojin nasu ba.

Sudan dai ta aika daruruwan sojoji zuwa Yaman domin yakar ‘yan tawayen Houthi ‘yan Shi’a da ke yi wa gwamnatin kasar bore.

 

Abdulkarim/TRT

SHARE

LEAVE A REPLY