An yi zanga-zangar adawar May a Ingila

0
47

Dubabban mutane sun taru a birnin Landan inda suka yi zanga-zangar wani hukuncin da ya kunshi kara haraji.

Wata kungiya da ake kira da Majalisar Jama’a ce ta shirya taron inda aka fara taron daga ofishin BBC zuwa ginin majalisar kasar da ke Westminster.

An yi taron ne domin nuna adawa ga hukuncin da ya kunshi kara haraji inda kuma jama’an suka nemi firaministan kasar da ta yi murabus.

Shugaban kungiyar siyasar hamayyar Masu Aiki Jeremy Corbyn ma ya halarci taron.

An yi zanga-zangar ne a layin da gidan firaminista ya ke.

Theresa May ta rasa jama’a a majalisa bayan zaben da aka yi a ranar 8 ga watan Yuni.

Theresa May tana burin kafa gwamnati a Arewacin Ayalan inda hakan ya sa ‘yan adawa da ma ‘yan kungiyar ta ta suka mata martani.

 

Abdulkarim/TRT

SHARE

LEAVE A REPLY