Asusun Kwankwasiyya ya tallafa wa kungiyoyin kwallon kafa a jihar Kano

0
803

Hukumar kula da wasannin kwallon kafa ta Najeriya NFF ta sha alwashin ci gaba da goyon bayan duk wata kungiya dake tallafa wa harkokin wasanni tsakanin matasa.

Jawabin hakan ya fito ne daga bakin jami’i a hukumar ta NFF Alh Ibrahim Gusau lokacin kaddamar da rarraba kayayyakin wasan kwallon kafa da kudade ga kungiyoyi dubu da Asusun Kwankwasiyya na tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya bayar a jihar Kano.

Wakilin Muryar Najeriya a Jihar Kano Tukur Garba ya rawaito cewa, Hukumar ta NFF ta ce samar da kayayyakin wasanni a matakin farko shi ne kadai zai taimaka wajen ci gaban fannin wasanni kamar yadda shugaban hukumar ta NFF Amaju Pinnick ya bayyana ta bakin jagoran shugaban hukumomin wasanni na  jihohi FA kana shugaban FA ta jihar Zamfara, Alh Ibrahim Gusau.

Yace “duk lokacin da mu ka ji wani mutum, jama’a ko kungiya  dama  gwamnatin dake son taimaka wa kungiyoyi kwallon kafar matasa na wannan kasa a shirye muke mu shiga ayi damu, domin tabbatar da ganin an tallafa wa wadannan matasa”

Da yake gabatar da nasa jawabin shugaban kwamitin shirye shirye karkashin asusun na Kwankwasiyya Hon Nuhu Danburan, bayyana abubuwan da taron ya kunsa yayi.

Kimanin Naira miliyan Dari da Hamsin ne wannan asusun ya kashe a wannan shiri, inda kungiyoyin kwallon kafa Dari Biyar a jihar kano suka amfana, kuma wasu Dari Biyar din daga jihohin arewacin Najeriya Goma Sha Tara zasu amfana nan bada jima wa ba.

Har-wa-yau asusun yace nan da zuwa watanni uku mai zuwa daukacin kungiyoyin kwallon kafa a jihohin Najeriya 36 da birnin Abuja zasu amfana da wannan shiri na Kwankwasiyya. Kayayyakin da aka rarraba sun hada da Riga (Jersey) da wando da safa harma da kwallon kafa (Ball) gami da kudade ga wadannan kungiyoyi.

Ga Tukur Garba Arab dauke da cikakken rahoto

 

Abdulkarim/Tukur G. Arab

SHARE

LEAVE A REPLY