Cutar Ebola ta kashe mutane 2 a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo

0
65

Mutane 2 ne suka mutu sakamakonkamu wa da cutar Ebola a kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da ke Tsakiya Afirka.

Dakta Charles Kaso da ke aiki a cibiyar lafiya ta garin Bas Uele ya bayyana cewa, an samu bullar cutar a kauyen Likati da ke garin.

Kaso ya kuma ce, cibiyar bincike kan magunguna ta kasar kuma ta ce, sun gwada jinin mutane 5 inda suka kuma gano cewa, suna dauke da cutar Ebola.

A cikin ‘yan kwanakin da suka gabata an samu mutane 10 da nuna alamun kamuwa da cutar inda 2 daga cikinsu suka mutu.

Ministan lafiya na kasar Oly Ilunga Kalnega ya ce, abin bakin ciki kasarsu ta sake kamuwa da cutar Ebola.

Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya ta fitar da sanarwa inda ta tabbatar da karbar bayanai daga wajen ministan.

A shekarar 1976 ne cutar Ebola ta fara bulla a kasar Kongo inda a shekarar 2013 ta yadu sosai a yammacin Afirka.

 

Abdulkarim/TRT

SHARE

LEAVE A REPLY