Dangantaka ta yi tsami tsakanin kasashen Amurka da Rasha

0
98

Ministan harkokin wajen Rasha, Sergey Lavrov, ya bayyana cewa Moscow na kokarin daukar matakan ramuwar gayya a wani yunkuri na maida martini a kan Amurka, sakamokon kwace wasu gine-gine na ofishin jakandancin Rasha.

Ministan harkokin wajen na Rasha ya ce Moscow ta yi shirin korar kimani jam’ian diflomasiyyar Amurka 30 tare da kwace gine-gine da abubuwa da dama mallakar ofishin jakadancin Amurka dake kasar Rasha.

Matakan da Amurka ta dauka a kan Rasha sun hada da hana shiga wasu gine-gine guda biyu mallakar ofishin jakadancin Rasha dake birnin Washington da kuma ofishin jakandincin Rasha a Majalisar dinkin duniya na dundundun da ke birnin New York.

Kasar Rasha ta musanta yin katsalandan a zaben shugaban kasar Amurka, inda ta dage kan cewa ba ta sa baki ba akan harkokin cikin gidan ko wace kasa.

Abdulkarim

SHARE

LEAVE A REPLY