Fadar shugaban kasa ta tabbatar da kara ceto wata daga cikin ‘yanmatan Chibok.

0
97
Yan Matan Chibok 82 da Boko Haram ta Sako
  1. Gwamnatin Najeriya ta ce wata yarinya daga cikin ‘yan matan Chibok da suka rage a hannun kungiyar Boko Haram ta tsere daga hannun kungiyar.Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan a wajen taron majalisar minsitoci a ranar Laraba.An yi amannar cewa wasu sojoji ne suka tsince ta a lokacin da tsere tana hanyar guduwa.
    Talla

    A cewar mai baiwa shugaban kasa shawara ta musanman kan harkokin yada lqbarai, Mista Adesina ya ce sai dai kuma ba a yi wani karin bayani kan ko wacece ita ba, ba kuma a fadi a halin da aka tsince ta ba.

    A ranar 6 ga watan Mayu ne kungiyar Boko Haram ta sako ‘yan mata 82 na makarantar sakandaren Chibok din, bayan sasantawar shiga tsakanin gwamnati da kungiyar Boko Haram din da wasu kungiyoyi da kasashe suka yi.

  2. Abdulkarim
SHARE

LEAVE A REPLY