FIFA da CAF sun taya Kanu murnar cika shekaru 41

0
8931

Hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA da ta Nahiyar Afrika CAF da kuma kungiyar kwalon kafa ta kasar Ingila Arsenal sun turo sakon taya murna ga tsahon dan wasan kungiyar Super Eagles Nwankwo Kanu na ciki shekaru 41 a duniya.

Hukumomin sun aiko da sakonninsu ne ta hanyar kafar sada zumunta na tweeter a ranar talatar nan.

Haka suma sauran kungiyoyin da tsohon dan wasan ya buga wa kamar su Ajax Amserdam, da Inter Milan sun aiko da nasu sakonnin.

Kanu dai ya bugawa kungiyar Ajax tun daga shekara ta 1994 zuwa 1996 inda ya taimaka mata samun nasarar cin kofuna da suka hada da kofin zakarun nahiyar turai a shekara ta 1995 da kofin UEFA Super Cup a shekara ta 1995 da kuma kofin Intercontinantal shi ma a shekara ta 1995.

Har ila yau Kanu na cikin jerin ‘yan wasan da suka sami nasarar cin kofin UEFA cup a kungiyar Inter Milan a shekara ta 1998

A kungiyar Arsenal ta kasar Ingila kuwa Kanu ya sami nasarar cin kofunan Premier League biyu a shekarun 2002 da kuma 2004 sannan sun kuma sami nasarar cin kofin FA a shekara ta 2002 da 2003. Ya kuma taimaka wa kungiyar kwallon kafa ta Portmouth ta kasar Ingila har ila yau wajan lashe kofin Premier League a shekara ta 2008 inda kwalon da ya zura wa kungiyar Cardiff City ne ya basu nasarar.

A wasanin da Kanu ya Bugawa kasar sa kuwa, a kungiyar kwallon kafa ta ‘yan kasa da shekaru 17, kanu sun ci kofin kwallon kafa na duniya na ‘yan kasa da shekaru 17 a shekara ta 1993 inda a shekara ta 1996 suka lashe lambar zinari a wasannin Olympic a kungiyar Golden Eaglets na ‘yan kasa da shekaru 23.

Har ila yau Kanu ya Bugawa kungiyar Super Eagles wasanni inda ya buga mata wasannin cin kofin kwallon kafa na duniya sau uku a shekara ta 1998 da 2002 da kuma 2010, sai kofin nahiyar Afrika inda ya buga sau 6 a shekara ta 2000 da 2002 da 2004 da 2006 da 2008 da kuma 2010.

Abdulkarim/Nura M

SHARE

LEAVE A REPLY