Gwamnatin Cross Rivers zata tallafa wa kanana da matsakaitan masana’antu

0
70
Mataimakin Gwamnan Jihar Cross Rivers, Farfesa Ivara Esu.

Mataimakin Gwamnan Jihar Cross Rivers, Farfessa Ivara Esu ya bayyana cewa jiharsa za ta samar da kyakkyawan yanayin kawasuwanci domin ci gaban kanana da matsakaitan masana’antu a cikin jihar.

Mataimakin Gwamman ne ya bayar da tabbacin hakan a garin kalaba yayin da ya karbi bakunci Tawagar shugabannin Kungiyar masu samar da ruwan sha na roba ta Najeriya reshen jihar Cross Rivers a ofishinsa.

Mataimakin gwamnan yace kanana da matsakaitan masana’antu na da mutukar mahimanci wajen ci gaban tattalin arzikin jihar, a saboda haka a kwai bukatar karfafa masu gwiwa domin kyautatta rayuwar al’ummma baki daya.

Farfessa Ivara Esu ya yi alkawarin cewa gwamnatin jihar za ta yi dukkan maiyuwa domin kawo karshen biyan haraji da yawa ga masu kanana da matsakaitan masana’antu.

 

Abdulkarim Rabiu.

SHARE

LEAVE A REPLY