Gwamnatin Najeriya ta dakatar da Shugaban hukumar Inshorar Lafiya (NHIS)

0
8772

Ministan Lafiya na Najeriya Isaac Adewale ya bayar da umarnin dakatar da shugaban hukumar kula da inshorar lafiya na kasar (NHIS), Usman Yusuf, bisa zargin da ake masa na wawure kudin hukumar.

Wani kwamitin Majalisar Dattawan kasar ne yake zargin Mista Yusuf da yin sama da fadi da dubban dalolin hukumar.

Mai magana da yawun ma’aikatar lafiyar Mrs Akintola shaida wa maneman labarai cewa an dakatar da shi ne na tsawon wata uku kafin a kammala bincike a kan zarge-zargen da ake yi masa.

Ta ce a ranar Alhamis ne ministan lafiya na Najeriya Isaac Adewole, ya bayar da umarnin a dakatar da shugaban NHIS din ba tare da bata lokaci ba.

Ta kara da cewa ana tuhumarsa, “a kan abubuwa daban-daban, amma ba zan iya tabbatar da ko akwai batun kudin hukumar ba” kamar yadda rahotanni suka nuna.

Majalisar Dattawan na tuhumar Mista Yusuf ne da kashe kudaden hukumar har kimanin naira miliyan 292 ba bisa ka’ida ba.

Mista Yusuf ya zama shugaban hukumar NHIS ne a watan Yulin shekarar 2016.

Gwamnati ta shawarci maaikatan hukaumar da su kasance masu bin doka da oda, tare da sanya ido da kuma lura da dukkan kadarorin gwamnati ciki kuwa har da mahimman takardu.

Abdulkarim

SHARE

LEAVE A REPLY