Gwamnatin Najeriya Za ta Gina Karin Matatar Mai a Jihar Rivers

0
145

Gwamnatin Tarayyar Najeriya hadin gwiwa da katafaren kamfanin mai na kasar Italiya AGIP, sun cimma yarjejeniyar gina matatar man fetur mai lita dubu dari da hamsin a jihar Rivers dake kudu maso kudancin Najeriya.

Ministan albarkatun man fetur Mr. Ibe Kachikwu ya sanar da hakan ranar talatar nan yayin da yake wa maneman labarai jawabin sakamakon taron tsakanin ma’aitakatar albarkatun man fetur da jami’an kamfanin na AGIP a fadar shugaban kasa.

Mr. Kachikwu ya kuma ce jumillar kudin da kamfanin na AGIP zai sanya jari da su a ginin matatar man da kuma sauran muhimman ayyuka, sun hada da ginin filin Zabazaba da gyaran matatar man ta garin Patakwal za su lakume karin dala miliyan 15.

Daga nan sai Ministan man ya bukaci sauran manyan kamfanonin kasashen waje dake Najeriya da su kwaikwayi kokarin kamfanin na AGIP musamman a bangarorin hasken lantarki, a filin da AGIP ke ginin tashar lantarki karo na 2 da ake sa ran kammala wa a tsakanin shekarun 2019 zuwa 2020.

 

Abdulkarim/Tsamiya

 

 

SHARE

LEAVE A REPLY