Gwamnatin Zamfara za ta sayar wa da manoma taki kan Naira 5,000

0
159

Gwamnatin Jahar Zamfara ta sayo ton dubu Hamsin (50,000 tons) na nau’in takin zamani daban daban, domin sayar wa manoma a kan farashin Naira Dubu Biyar (=N=5,000.00) ga ko wane buhu daya na nau’in takin zamanin.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin kwamishina mai Kula da ma’aikatar aikin gona ta Jahar Zamfara, Injiniya Lawal Jibirin Jangebe a zantawarshi da Muryar Najeriya a ofishin ma’aikatar aikin gona ta Jahar dake birnin Gusau.

Injiniya Jangebe ya bayyana cewa, gwamnatin Jahar ta nada kwamitin amintattun mutanen da ta dorawa nauyin sanya idanu akan yadda za’a sayar wa manoma takin zamani a kan farashin da gwamnatin Jahar ta kayyade.

Yace a halin yanzu an kaddamar da sayar wa manoma takin zamani kashi na farko, yayin da za a soma sayar masu kaso na biyu a cikin makwanni masu zuwa.

Da juya a kan matakan da gwamnatin Jahar ta dauka na sayar wa manoman dake zaune a yankunan karkara kuwa, injiniya Jangebe ya yi bayanin cewa, an kaddamar da kwamitin amintattun mutane a matakin majalisun kananan Hukumomi da gundumomin iyayen kasa domin ganin cewa kason takin ya isa ga dukkan manoman dake cikin jahar.

Ya kuma shawarci manoma da su gaggauta yin amfani da wannan takin da suka saya kashi na farko kafin lokacin da za a yi zagaye na biyu anan gaba.

Ga rahoton Hamisu Danjiba daga Birnin Gusau

Abdulkarim Rabiu/Hamisu Danjiba

 

 

 

 

 

 

SHARE

LEAVE A REPLY