Gwamnonin arewa za su bada tallafi wajen gina hedikwatar JIBWIS a Abuja

0
610

Gwamnatocin jahohin Arewa maso yammacin Najeriya sun yi alkawarin bada gudun mawar da ya kamata, wajen kammala aikin ginin ci biyar yada addinin Islama wanda Kungiyar izalatul Bidi’ah wa Ikamatis sunnah ta Najeriya mai Hedikwata a Jos take gudanarwa a garin Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin, mataimakin shugaban kungiyar na  Najeriya, shaihin malami Yusufu Sambo Rigacukum, a lokacin da ya ke yi wa shugabanni da wakilan  kungiyar na jahar Zamfara bayani a garin Gusau.

Shaihin Malami Yusufu Sambo, wanda Hedikwatar kungiyar ta Najeriya ta bai wa shugaban cin kusoshin kungiya, an dora masu nauyin zagaya jahohin Arewa maso yamma cin Najeriya, domin neman tallafin kudi ko kayan aiki domin Kammala aikin ginin wannan ci biyar yadda addinin Islama da kungiyar ke gudanar wa a birnin Abuja.

Ya kuma yi bayani akan irin gagarumar Nasarar da ayarin nasu ya samu a lokacin da ya ziyarci jahohin kano da Kaduna da Jigawa da kuma katsina.

Har ila yau kuma shugaban ya bayyana irin gudunmawar da ake bukatar rassan kungiyar a matakin jahohi da kananan hukumomi zasu bada domin samun nasarar kammala wannan aikin na ginin cibiyar yada addinin Islama, yayin da ya ce suna kan shirin kafa tashar Rediyo da Talabijin mallakar wannan kungiyar a birnin Abuja.

Ga Hamisu Danjibga dauke da cikakken rahoto.

LEAVE A REPLY